Mutane Kusan 300 Isra’ila Ta Kashe A Farmakin Khan Yunis

Hukumar kare fararen hula ta Gaza ta ce farmakin da Isra’ila ta kai a Khan Yunis da kewaye ya kashe mutane kusan 300 a cikin

Hukumar kare fararen hula ta Gaza ta ce farmakin da Isra’ila ta kai a Khan Yunis da kewaye ya kashe mutane kusan 300 a cikin ‘yan kwanakin nan.

Kakakin hukumar Mahmud Bassal ya fada a ranar Talata cewa adadin shahidai a Khan Younis ya zarce yadda aka yi tsammani tun farko, inda aka tabbatar da kashe mutane akalla 300 da sojojin Isra’ila suka yi.

Hukumar ta zargi sojojin Isra’ila da hana daukar wadanda suka jikkata, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsu da kuma bazuwar gawarwakinsu.

Adadin wadanda suka mutu na iya zarce haka, duba da rahoton bacewar Falasdinawa 200 a gabashin Khan Yunis.

“Ma’aikatanmu na ci gaba da neman wadanda suka bace,” in ji shi.

An jefa bama-bamai a gidaje da dama yayin da Falasdinawa ke zaune.

A yanzu haka Falasdinawa na komawa Khan Yunis bayan farmakin da Isra’ila ta kai musu na tilasta musu hijira a makon da ya gabata.

lamarin ya raba akalla Falasdinawa 180,000 a cikin kwanaki hudun farko, inda aka tilastawa da yawa barin kayansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments