Pezeshkian, Ya Yi Rantsuwar Kama Aiki A Matsayin Shugaban Iran Na 9

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya yi rantsuwar kamai aiki a gaban majalisar dokokin kasar, a bikin da aka shirya tare da halartar manyan baki da

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya yi rantsuwar kamai aiki a gaban majalisar dokokin kasar, a bikin da aka shirya tare da halartar manyan baki da yammacin yau Talata.

Bayan shan rantsuwa bisa kur’ani mai tsarki, Pezeshkian ya lashi takobin kare addinin musulunci da na Jamhuriyar Musulunci da kuma kundin tsarin mulkin kasar.

“A matsayina na shugaban kasa, a gaban kur’ani mai tsarki da kuma gaban al’ummar Iran, ina rantsuwa da Allah Madaukakin Sarki cewa, zan kiyaye addini a hukumance, da tsarin Jamhuriyar Musulunci, da kuma kundin tsarin mulkin kasar.”

Pezeshkian ya kara da cewa “Zan sadaukar da dukkan iyawa da cancantata don sauke nauyin da aka dora mini, kuma zan dukufa wajen yi wa jama’a hidima da daukaka al’umma, inganta addini da dabi’u, goyon bayan adalci, da fadada adalci.”

A jawabinsa nasa na farko bayan rantsar da shi, Pezeshkian ya bukaci duniya da ta yi amfani da “wannan dama mara misaltuwa” don yin aiki tare da Iran wajen tinkarar kalubalen yankin da na duniya baki daya.

Shugaban ya yi alkawarin kare martaba da muradun Iran a duniya, a matsayin ginshikai uku na manufofinsa na ketare.

Shugaban ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa wajen ganin an dage takunkumin da kasashen yamma suka kakaba Iran. “Ina ganin daidaita dangantakar tattalin arziki da kasuwanci da Iran da kasashen duniya a matsayin hakki na Iran, kuma ba zan gajiya ba har sai an dage takunkumin da aka sanya mata na rashin adalci.”

Ya kuma bukaci tsayin daka domin kawo karshen zalincin da ake yi wa al’ummar falasdinu.

Share

2 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments