Iran: Fadada Wuraren Da HKi Take Kai Wa Hare-hare Bazarana Ce Ga Tsaron Duniya

Babban jami’in diplomasiyyar Iran Ali Bakiri Kani ne ya bayyana  haka, yana mai kara da cewa; Cigaba da fadada laifukan HKi a yankin Gaza, wata

Babban jami’in diplomasiyyar Iran Ali Bakiri Kani ne ya bayyana  haka, yana mai kara da cewa; Cigaba da fadada laifukan HKi a yankin Gaza, wata babbar barazana ce ga sulhu da zaman lafiya na duniya.

Babban jami’in diplomasiyyar ta Iran ya bayyana haka ne a yayin da ya gana da  mataimakin minstan harkokin wajen kasar Cuba.

Bugu da kari, babban jami’in diplomasiyyar na Iran ya yi ishara da yanayin da ake ciki a Gaza na barnar da HKI take yi da kuma laifukan da take tafkawa akan al’ummar Falasdinu,tare da wannan shi ne batu da ya fi kowane muhimmanci a duniya ta fuskar ‘yan’adamtaka.

Har ila yau Bakiri Kani, ya ce, cigaba da aikata wannan irin danyen laifin yana nufin; Aikata laifi akan jinsin bil’adama,kuma nauyi ne wanda ya rataya a wuyanmu na ganin an kawo karshen wannan laifin.

Shi dai mataimakin ministan harkokin wajen kasar Cuba tare da wata tawaga sun iso Iran ne domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasa Mas’ud Fizishkiyan wanda za a yi a gobe Talata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments