Iran Ta Musanta Zargin Da Kasashen Amurka Burtaniya Da Kuma Faransa Suke Mata

Jakadan kasar  Iran a MDD ya rubutawa babban sakataren MDD wasika inda yake maida martini kan tuhumar da kasashen Amurka, Burtania da faransa sukewa kasar,

Jakadan kasar  Iran a MDD ya rubutawa babban sakataren MDD wasika inda yake maida martini kan tuhumar da kasashen Amurka, Burtania da faransa sukewa kasar, na cewa ita ta rikita yankin gabas ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Amir Saeed Iravani yana fadar haka a cikin wasikar ya kuma kara da cewa wadannan kasashen uku sun dauki wannan matakin a kan Iran ne don kauda hankalin duniya daga irin ta’asar da HKI take aikatawa a Gaza.

Kafin haka dai, jakadun wadannan kasashe uku sun zargi kasar Iran da taimakawa kasar Yemen da makamai wadanda ta kai hare hare masu tsanani dasu a tsakiyar birnin Tel aviv babban birnin HKI a makon da ya gabata.

Wadannan kasashe sun yi haka ne, ba tare da la’akari da irin ta’asan da HKI take aikatawa a gaza ba, inda ya zuwa yanzu akalla falasdinawa kimani 40,000 ne, mafi yawansu mata da yara ne suka rasa rayukansu. HKI tana samun makaman da take wannan kissan kiyashi ne daga wadannan kasashe uku da kuma wasu kasashen turai.

Labarin ya kara da cewa wasikar wacce ta isa hannun Antonio gutorres a jiya Talata, har’iala yau ta isa hannuna shugaban kwamitin tsaro na majalisar.

Wasikar ta kara da cewa wadannan kasashe 3 sun yi shiru a kan dukkan ayyukan kissan mutanen da hki take yi a gaza da kuma sauran kasashen yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments