Wata sanarwa da hukumomin Asibitin Al Awda suka fitar ta ce an kai gawawwaki huɗu da kuma mutane da dama da suka jikkata sakamakon harin da Isra’ila ta kai ta sama a wani gida da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat.
Rundunar Tsaron fararen-hula ta Gaza ta aike da saƙo ta manhajar Telegram cewa an kashe Falasɗinawa shida sannan aka jikkata wasu da dama a wani luguden wuta da sojojin Isra’ila suka yi a gidansu da ke sansanin Bureij.
Kawo yanzu ba a san takamaimai adadin mutanen da aka kashe ba.
Saƙon ya ƙara da cewa tawagar rundunar tana ci gaba da aiki don zaƙulo mutanen da ɓaraguzai suka binne.
Ganau sun shaida wa Anadolu cewa jiragen ruwan yaƙin Isra’ila sun rusa gidaje biyu— gidan iyalan Gharab a sansanin Nuseirat da gidan iyalan Khalifa a sansanin Bureij.