Jagora ya yi kira da a yi mu’amala mai ma’ana’ tsakanin majalisa da sabuwar gwamnati

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce nasarar da sabon zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian wajen gudanar da ayyukansa nasara ce ta dukkanin al’ummar Iran. Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da ‘yan majalisar sabuwar majalisar dokokin kasar Iran a yau Lahadi a birnin Tehran. […]
Kungiyar EU ta ce tana goyon bayan hukuncin ICJ da ta yanke kan Isra’ila

Babban jami’an kungiyar Tarayyar Turai kan Harkokin Waje ya yaba da shawarar da Kotun Duniya (ICJ) ta bayar game da Isra’ila. Josep Borrell ya ce gabatar da wadannan shawarwarin ya yi daidai da matsayin kungiyar Tarayyar Turai da kuma kudurorin Majalisar Dinkin Duniya dangane da matsayin yankunan Falasdinawa da Isra’ila mamaye. “A cikin duniyar yau […]
Isra’ila na ci gaba da kaddamar da hare-haren kisan kare dangi a Gaza

Wata sanarwa da hukumomin Asibitin Al Awda suka fitar ta ce an kai gawawwaki huɗu da kuma mutane da dama da suka jikkata sakamakon harin da Isra’ila ta kai ta sama a wani gida da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat. Rundunar Tsaron fararen-hula ta Gaza ta aike da saƙo ta manhajar Telegram cewa […]
Rundunar Sojin Yeman ta kaddamar da sabbin hare-hare masu girgizawa kan Isra’ila da Amurka

Dakarun Yaman sun kai farmaki guda biyu, daya ya nufi wani birnin da Isra’ila ta mamaye, daya kuma a kan wani jirgin ruwan Amurka a tekun Bahar Maliya. Dakarun na Yemen sun kai wani samame na sojan sama a kan muhimman wurare a Umm al-Rashrash [Eilat] da makamai masu linzami da dama, tare da cimma […]
Kungiyar Hamas ta yi maraba da bayyana Netenyahu a matsayin dan ta’adda da kasar Pakistan ta yi

Bayanin da kungiyar ta Hamas ta fitar ya kunshi cewa; muna yin maraba da lale da bayanin da ya fito daga gwamnatin Pakistan wacce ta dauki yan sahahyoniya a matsayin masu tafka laifuka shi kuma Netenyahu a matsayin dan ta’adda. Har ila yau, kungiyar ta Hamas ta ce, matakin da Pakistan din ta dauka wani […]
Ana Cigaba Da Yin Tir Da Hare-haren Da HKI Ta Kai Wa Kasar Yemen

Kakakin Ma’aiakatar harkokin wajen Iran ya yi tir da harin da jiragen yakin HKI su ka kai wa kasar Yemen, yana mai cewa; An kai wa mutanen na kasar Yemen hari ne saboda suna kare daukaka da izza da mutuncin mutanen Gaza mata da kananan da ake yi wa kisan kiyashi. Dr. Nasir Kan’ani wanda […]
A Kalla Falasdinwa 11 Ne Su Ka Yi Shahada Da Safiyar Yau Lahadi

A cigaba da kai hare-hare na wuce gona iri da HKI take yi, da safiyar yau sun kai hari da jiragen yaki akan yankin Gaza da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 11. Jiragen yakin HKI sun kai harin ne akan wani rukunin gidaje dake sansanin ‘yan hijira na “ Alburaij’ da kuma Nusairat’ wadanda […]
Zababben Shugaban Kasar Iran Ya ce; Aikin Da Yake Gabansa Shi Ne Warware Matsalolin Al’umma

Zababben shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda ya gana da ‘yan majalisar shawarar musulunci ta Iran, ya bayyana cewa; Abinda ya kawo mu shi ne lalubo hanyoyin da za a warware matsalolin al’umma. Mas’ud Fizishkiyan ya kuma kara cewa; Na sha fada ina nanatawa a yayin muhawar yakin neman zabe da kuma a wannan majalisar […]
Yemen : A Shirye Muke Shiga Dogon Yaki Da Isra’ila, Bayan Harin Hodeidah

Dakarun Yemen sun lashi takobin ci gaba da gudanar da ayyukansu na goyon bayan Falasdinawa bayan da gwamnatin Isra’ila ta kai hare-hare kan cibiyoyin fararen hula a lardin Hudeidah. Kakakin rundunar Birgediya Janar Yahya Saree ya bayyana, sa’o’i bayan da jiragen yakin Isra’ila suka kai harin cewa a shirye su ke domin shiga dogon yaki […]
Iran Ta Soki Harin Isra’ila A Yemen, Tana Mai Gargadin Hakan Zai Kara Rura Wutar Rikici A Yankin

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren da Isra’ila ta kai kan yammacin kasar Yemen, inda ta yi gargadin cewa irin wannan ta’addancin na iya kara tsananta halin da ake ciki a yankin. Kakakin ma’aikatar Nasser Kan’ani, ne ya bayyana hakan, sa’o’i bayan da jiragen yakin Isra’ila suka kai […]
Najeriya Ta Ci Tarar Facebook Da WatsApp $ 200M Kan Karya Dokar Kare Sirrin Mutane

Hukumar kare hakkin kwastomomi ta tarayyar Nijeriya ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 220 saboda samun manhajojinsa na Facebook da WhatsApp da laifin keta dokar kare sirrin masu amfani da su a kasar. A wata sanarwa da Hukumar Nigeria Competition and Consumer Protection Commission (FCCPC) ta fitar ranar Juma’a, ta ce binciken hadin-gwiwa da […]
Martanin Kasashen Duniya Kan Hukuncin ICJ, Ga Mamayar Da Isra’ila Ke Wa Falasdinu

Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani game da matakin kotun duniya ta ICJ ga Isra’ila na ta gaggauta dakatar da ayyukanta na mamayar yankunan Falasdinawa a Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma Gabashin Kudus, wanda ta kira da “haramtattu.” Masarautar Saudiyya ta yi maraba da hukuncin yayin da ta jaddada “bukatar […]
Guterres Ya Nuna Matukar Damuwa Game Da Harin Isra’ila Kan Yemen

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteress, ya nuna matukar damuwa game da harin da Isra’ila ta kai a lardin Hodeidah na kasar Yemen. Mista Guterres, ya bayyana matukar damuwarsa kan hare-haren Isra’ila a tashar ruwan Hodeidah da ke Yeman, a cewar wata sanarwa da aka aike wa ‘yan jarida. “Sakataren Janar ya yi kira […]