Babbann hafsan hafsoshin sojojin HKI ya bukaci firai ministan haramtacciyar kasar Benyamin Natanyahu ya sanya hannu a yarjeniyar musayar fursinoni da kungiyar Hamas.
Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto shafin yanar gizo labarai da harshen Ibranci ‘Illo’ Yana fadar haka. Labarin ya kara da cewa bayan mintuna kimani 30 da fara taro da manya manyan sojojin kasar sai babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Herzi Halevi ya bukaci Natanyayu ya sanya hannu kan yarjeniyar tsagaita wuta da Hamas daga ciki hard a musayar Fursinoni da ita.
Halevi ya kara da cewa sanya hannu a yarjeniyar zai taimakawa HKI kaiwa ga manufofin ta a yakin da ta shiga da kungiyar Hams. Kafin wannan taron dai Natanyahu ya je garin Rafah na yankin Gaza inda ya fadawa sojojinsa da suke fafatawa da Hamas kan cewa su kara hakuri su kuma ci gaba da yakar kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin Falasdinawa har zuwa nasara. Ya kuma ya masu alkawalin nasara tana kusa.