Saudiyya Da Iran Sun Jadadda Mahimmancin Karfafa Alaka Tsakaninsu

Kasashen Saudiyya da Iran sun jadadda mahimmancin karfafa alaka a tsakaninsu. Wannan bayyanin ya fito a yayin wata zantawa ta wayar tarho tsakananin Mohammed bin

Kasashen Saudiyya da Iran sun jadadda mahimmancin karfafa alaka a tsakaninsu.

Wannan bayyanin ya fito a yayin wata zantawa ta wayar tarho tsakananin Mohammed bin Salman, yarima mai jiran gado na Saudiyya, da Masoud Al-Madijian, zababben shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda suka jaddada muhimmancin bunkasa hadin gwiwa tsakanin Tehran da Riyadh.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da Masoud Pezeshkian, bin Salman ya sake taya Pazeshkian murnar nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar Iran karo na 14, tare da fatan samun ci gaba da wadata ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Yarima mai jiran gado na Saudiyya ya ce Riyadh na son fadada da zurfafa alakar kasashen biyu a fannoni daban daban.

Shi ma zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya nuna jin dadinsa ga yarima mai jiran gadon sarautar kasar Saudiyya.

Bangarorin biyu sun kuma jaddada bukatar bunkasa hadin gwiwa tsakanin Saudiyya da Iran a fannoni daban-daban.

Inganta da kuma karfafa alaka tsakanin Iran da Saudiyya a cikin ‘yan shekarun nan, musamman a gwamnati ta 13 ta marigayi shugaban kasa Ebrahim Ra’isi da kuma ministan harkokin wajen kasar Iran mai shahada, ya kasance daya daga cikin muhimman manufofin harkokin wajen kasar, kuma kamar yadda ya zo daga Bayanin jami’an kasashen biyu, bangarorin biyu suna da matukar sha’awar kiyaye wannan alaka domin moriyar juna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments