Pezeshkian : Zamu Maida Hankali Kan Fadada Dangantaka Da Ketare

Zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa, babbar hanyar manufofin ketare na sabuwar gwamnatin kasar ita ce bude sabbin dabaru da fadada dangantakar

Zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa, babbar hanyar manufofin ketare na sabuwar gwamnatin kasar ita ce bude sabbin dabaru da fadada dangantakar abokantaka da sauran gwamnatoci bisa tattaunawa, hadin gwiwa, daidaito da mutunta juna.

Da yake nuna godoya game da sakonni na taya shi murna da ya samu daga kasashe fiye da 40, zababben shugaban kasar ta Iran ya jaddada cewa, babbar hanyar da sabuwar gwamnatinsa za ta bi wajen kulla huldar diplomasiyya, ita ce bude sabbin dabaru na fadada huldar abokantaka da sauran gwamnatoci gaba daya.

Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta mai da hankali sosai wajen kara zurfafa alaka tsakaninta da gwamnatoci na kasashe makwabta, na yankin da sauran gwamnatoci dama a duk inda zai yiwu.

Ya zuwa yanzu, zababen shugaban kasar ta iran Mr. Pezeshkian ya samu sakonni da kiraye kiraye waya na taya shi murna daga shugabanni da gwamnatocin kasashe fiye da arba’in.

A ranar 30 ga watan nan ne ake sa ran rantsar da Pezeshkiana matsayin sabon shugaban kasar ta Iran da zai maye gurbin shahid Ebrahim Ra’isi, da ya yi shahada a mummunan hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar 19 ga watan Mayun tare da wasu mukarabansa ciki har da ministan harkokin wajen Kasar Hossein Amir Abdolahian.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments