Saudiyya: Alhazai fiye da dubu da dari uku ne suka rasu a Hajjin bana

Hukumomi a Saudiyya sun ce alhazai sama da 1,300 ne suka mutu lokacin Hajjin bana wanda aka gudanar a yanayi na tsananin zafi, kuma yawancin

Hukumomi a Saudiyya sun ce alhazai sama da 1,300 ne suka mutu lokacin Hajjin bana wanda aka gudanar a yanayi na tsananin zafi, kuma yawancin waɗanda suka mutu ba su da takarda ta izinin yin aikin na Hajji.

“Abin takaici shi ne, mutanen da suka mutu sun kai 1,301, kuma kashi 83 daga cikinsu sun zo aikin Hajji ne ba tare da izini ba inda suka yi tafiyar-ƙafa mai tsawo cikin tsananin zafin rana, ba tare da makwanci ko kulawa ba,” in ji wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Saudiyya Saudi Press Agency ya bayar ranar Lahadi.

Wasu bayanai da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tattara a makon jiya, bisa ƙididdigar da hukumomi suka yi da kuma alƙaluma daga jami’an diflomasiyya na ƙasashen da suka tura jama’arsu Hajji, sun nuna cewa alhazan da suka mutu sun kai 1,100.

Alhazan da suka rasu sun fito ne daga ƙasashe fiye da 10 daga Amurka zuwa Indonesia, kuma wasu gwamnatoci suna ci gaba da sabunta alƙaluman ‘yan ƙasashensu da suka rasu.

Jami’an diflomasiyya na ƙasashen Larabawa sun shaida wa AFP a makon jiya cewa ‘yan ƙasar Masar guda 658 ne suka mutu — kuma 630 daga cikinsu ba su yi rajistar aikin Hajji ba.

Jami’an na diflomasiyya sun ce yawancin mutanen sun rasu ne sakamakon tsananin zafi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments