Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadi game da barkewar rikici a yammacin Asiya bayan da Isra’ila ta yi barazanar kaddamar da farmaki a Lebanon.
Da yake zantawa da manema labarai a birnin New York, babban jami’in na MDD ya ce hadarin da ke tattare da rikici a yankin na kara fadada, yana mai nuni da yadda ake ci gaba da yin musayar wuta a kullum da musayar zafafen kalamai tsakanin gwamnatin Isra’ila da kungiyoyin ‘yan gwagwarmaya.
“Tilas a yau in bayyana matukar damuwata game da ci gaba da tabarbarewar da ake samu tsakanin Isra’ila da Hizbullah a yankin Blue Line.
Babban jami’in na Majalisar Dinkin Duniya ya ce al’ummar yankin da duniya baki daya ba za su bari ” Lebanon ta zama wata Gaza ba.”
Dole ne a kare fararen hula, bai kamata a kai hari ga yara ba, ‘yan jarida da ma’aikatan kiwon lafiya ba, kuma al’ummomin da suka rasa matsugunansu dole ne su koma gidajensu.