Majaliyar labaran soji ta kasar Yamen ta yi gargadi ga masu zuba hannayen jari na kasa da kasa cewa kayayyakin aiki na kamfanin mai na Aramco yana daga cikin wuraren da ba su da tsaro daga hare haren dakarun kasar yamen don haka duk wani sanya hannun jari a wajen tamkar caca ce kuma ya shirya tafka mummunan asara
A rahoton da kamfanin dillancin labarai na Saba News ya fitar ya sake jaddada gargadin da dakarun sojin kasar yamen suka yi ga dukkan kamfanonin zirga zirgan jiragen sama na yin amfani da sararin samaniyar kasar Saudiya, domin kaucewa afkuwar hare hare, amma banda sararin samaniyar biranen makka da madina.
Yace kamfanin mai na Aramco ya zama halastacen wajen da za’a kai ma hari, kuma ci gaba da saka hannun jari yana nunawa masu sanya jari da sauran sassan dake da alaka da shi ga asarar kayayyaki masu yawa adaidai lokacin da sojojin yamen ke ci gaba da nuna jajaircewarsu kan hare haren da saudiya ke kai musu