Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya fadi cewa suna ci gaba da tuntubar juna ta hanyar diflomasiya da kasar Qatar mai shiga tsakani game da bukatun kasar iran kan batun bude mashigar Hormuz ,ya jaddada cewa babu batun ganawa ta kai tsaye tsakaninsu da wakilan Amurka acikin ajendar
Ministan yayi wannan bayanin ne a gefen taron da yayi da kwamitin kula da tsaron kasa da tsarin siyasar waje na majalisa a jiya lahadi, inda yace babban jami’in diflomasiyar iran yayi tafiya zuwa kasar Qatar domin ci gaba da tattaunawa bayan ziyarar baya- bayan nan da wakilan kasar Qatar suka kawo nan birnin Tehran
Yace amma babu wata ganawa da wakilan Amurka a cikin lamarin, kuma babu wanda yake da shirin haka, yace iran a halin yanzu tana tattaunawa kan bukatun da ta gabatar ne ta hanyar masu shiga tsakani, kuma tattaunawa tana gudana ne kan batun mashigar Hormuz na kwanaki 7 inda iran ta amince ta bude amma na kwanaki 2, gwargwagwadon yadda kasar Qatar tayi na ganin an amince da sharudan kasar iran
Ministan harkokin wajen yace iran zata ci gaba da bin hanyoyin diflomasiya kuma ya nuna fatansa na ganin daya bangaren zai nuna hikma da aiki da gaskiyar lamarin yadda zasu fifita tattaunawa akan sauran zabubbukan