Iran: Wasu Tankokin Mai Biyu Da Suka Taka Doka Sun Fashe

jagoran IRGC yace wasu tankokin mai guda biyu da suka saba doka sun fashe a mashigar hormuz

Ofishin hulda da jama’a na dakarun kare juyin musulunci na kasar iran ya bayyana cewa sojojin ruwa na dakarun sun sanar cewa wasu jiragen ruwan mai guda biyu da suka taka dokokin shige da fice da aka shinfida sun fashe bayan da suka ci karo da nakiyoyin da aka da sa, a lokacin da suke kokarin bin hanyoyin da aka hana sai da izinin a mashigar hormuz

kamar yadda aka bayyana a daren jiya lahadi daya daga cikin jiragen ruwan babban jirgi ne mai daukar mai kuma yanzu haka yana ci da wuta bayan ya fashe  sakamakon bin hanyar da aka hana amfani da ita sai da izini

Haka zalika sun bayyana cewa dukkan jiragen ruwa guda biyu da gangan suka kashe duk wasu na’urar kan hanya da tsarin radarsu domin satar hanya su wuce a kudancin mashigar hormuz ,bisa goyon bayan sojojin taadda na Amurka lamarin da ya haddasa afkuwar hadarin da yasa jiragen suka tsaya cak a wajen

Dakarun IRIGC sun jaddada cewa jiragen ruwan da suka yi kunnen uwar shegu da gargadin da aka yi , suka shiga hanyoyin dake da hadari acikin ruwa to sun keta dokokin da kasar iran ta gindaya ne , kuma zata fuskanci sakamako mara dadi,kuma alhakin hakan ya doru akan masu jiragen ne, da suka zabi kin bin umarnin tsarin da masu kula da shige da fice na iran suka bayar

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted