Iran Yayi Tir Da Ikirarin UAE Da Kanada Kan Ikirarin Tsibirai A Iran

iran tayi tir da ikirarin da hadaddiyar daular larabwa da kanada suk yi game da mallakar tsibirin iran guda 3

Isma’ila Bagha’i kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran yayi kakkausar suka game da sanarwar hadin guiwa da hadaddiyar daular larabawa da kasar kanada suka fitar game da tsibirai guda 3 na kasar Iran wato Abu Musa da tambu babba da tambu karami dake tekun fasha

A cikin bayani da ya wallafa a shifinsa na X Bagha’I ya bayyana ikirarin da hadaddiyar daular larabawa tayi a matsayin abin dariya  da kuma shawarar da kasar kanada ta yanke a matsayin gajeriyar fahimta kuma sabanin kaidojin yarjejeniyar majalisar dinkin duniya

Yace an kafa hadaddiyar daular larabawa ne a shekara ta 1971 amma duk da wannan bayani na tarihi da ake da shi , da hujjoji na taswirar kasa, tana ci gaba da ikirari kan tsibiran kasar iran guda 3,wanda tarihi ya tabbatar da su a cikin wani bangare ne na kasar iran tsawon shekaru kafin kafa hadaddiyar daular larabawa.

A farkon makon nan ne fira ministan kasar kanada Mark carney da shugaban hadaddiyar daular larabawa shaikh khalid bin mohammad bin zayen al nahyan suka fitar da bayanin hadin guiwa na kira da akawo karshen abin da suka kira mamaya kan tsibirai guda 3, inda suke zargin cewa hakan ya sabawa ikon mallakar kasa na hadaddiyar daular larabawa da ma kaidojin majalisar dinkin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted