Kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta yi mummunan suka game da mataken sojo da sojojin HKI Suke dauka a garin Al-khali da sauran yankuna dake gabar yammacin kogin jodan, kuma ta bayyana matakin rusa gidaje da korar falasdinawa a matsayin wani aiki na cutar da falasdinawa fararen hula dake zaune a yankunan
A cikin wani bayani da ta fitar a jiyar jumaa Hamas ta ce daga cikin matakin da take dauka a Khalil a kwai karbe ikon kula da shige da fice a yankin, da kai samame a gidaje da kuma tilastawa iyalai falasdinawa barin gidajensu ba shiri, wanda hakan ya sabama dokokin kasa da kasa kuma keta hakkin dan adam ne
Kungiyar Hamas ta yi kira ga majalisar dinkin duniya da sauran hukumomi na kasa da kasa na kare hakkin dan adam da su shiga cikin lamari da gaggawa domin dakatatar da ci gaba da rushe- rushe da korar falasdinawa da isara’ila ke yi
kuma wannan bayani ya zo ne bayan da sojojin isara’ila suka rushe wasu gidaje mallakin wasu falasdinawa a jiya jumaa wanda suka kai wani hari da yayi sanadiyar halakar sojojin isara’ila guda biyu