Iran: Kasashen Turai Suna Biyan Farashin Yakin Amuka Kan Iran

babban sakatare majalisar tsaron kasa yace kasashen turai suna biyan farashi mai tsada sakamakon goyon bana taasar isra'ila

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasa major janaral muhsen Reza’I ya shaidawa gwamnatincin kasashen turai cewa yanzu suna biyan farashi mai tsada na irin goyon bayan ayyukan ta’addancin da gwamnatin  HKI ke yi , inda kasashen turai ke kokawa game da mummunan asarar da suka ayi ta biliyoyin yuro da ya jefa su cikin matsalar tattalin arziki sakamakon yakin da aka kaddamar kan iran

A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X Reza’I ya bayyana cewa kamar jiya ne kasashen turai suke alfahari da muggan ayyukan da gwamnatin sahyuniya take aikatawa, amma a yau kuma suna kokawa game da mummunar asarar da suka samu ta biliyoyin yuro da yakin iran ya jefa su a ciki, yace lokacin da kuke karfafa laifukan yaki  shin baku yi tunanin cewa sakamakon hakan zai iya shafarku ba, yaki da ta’addanci yana da tsada , yanku kuma lokacinku ne na biyan farashi

Wannan bayani yana zuwa ne bayan da  gwamnatocin kasashen turai ke kokawa game da iran tsadar rayuwa da yakin ya haifar, a ranar juma da ta gabata wani jigo a siyasar kasar jamus ya fadi cewa karuwar farashin makamashi dake da alaka da yakin ya jawo wa turai asarar da ta haura dala biliyan 112 cikin watannin 8 da suka gabata, don haka ya bukaci a nemi mafita ta hanyar diflomasiya

Ana su bangaren yan majalisar kungiyar tarayyar turai suna ci gaba da zargin Washington da tel aviv wajen kara zurfafa rikici , yayin da ita kuma kasar Brussel take kallon lamarin ta wata mahanga ta daban.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted