Sakataren baitul malin kasar Burtania ya yi gargadi kan matsalolin da kasar zata shiga ciki idan tsadar kayaki ya ci gaba a kasar, ya kumakara da cewa suna aiki tukuru don kawo karshen yaki da kuma dawo da zirga zirgan makamashi a yankin gabas ta tsakiya.
Tashar talabijan ta Al-mayadeentv ta kasar Lebanon ta nakalto John Haley yana fadar haka a yau Laraba ya kuma kara da cewa, kasar Burtania tana fama da tsadar makamashi wanda kuma yaketakurawa rayuwar Jama’a. John Haley ya kara da cewa idan wannan halin ya ci gaba yana iya shafar tsarin kasafin kudin kasar gaba daya wanda zai rikta al-amura da dama.
Ya ce tsadar gas da manfetur saboda rufe mashigar ruwa ta Hurmuz da Iran ta yi ya yi tasiri sosai a cikin al-amuran tattalin arziki na kasar Burtania, kuma idan ya kara dadewa zai yi lahani mai yawa ga al-amuran tattalin arziki da kuma rayuwar mutanen burtania.
Yace a farkon yakin dai gangar mai ya tashi daga dala 70 zuwa fiye da 100, sannan gas kuma ya cillawa har zuwa ninki uku na farashin a cikin watan Fabrayrun da ya gabata.