Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, duk wani sabon harin da HKI zata fara a yankin tekun farisa zai kara dagula al-amura a kasuwar makamashi a duniya.
Tashar talabijan ta Presstv a nan tehran ta Nakalto Aragchi yana fadar haka a jiya Talata a shafinsa na X a dai dai lokacinda ake taron kasashe masu zarzikin gas a duniya a birnin Mosco na kasar Rasha.
Ya ce idan wasu sabon yaki ya sake barkewa a tekun farisa, to akwai matsaloli masu yawa na karancin makamashi a kasuwanninsa a duniya, kuma masu cutarwa ne ga masu sayarwa da kuma masu saya.
Ya ce siyasar makamashi na Iran ya ci gaba sosai a taron kasashe masu arzikin gas a duniya wato GECF wanda aka gudanar a birnin Mosco. Inda kasashen suka tattauna dangane da kasuwar gas da kuma tsaro.
A taron wanda aka gudanar a jiya Talata, ya bawa kasashen Iran da Rasha damar tattaunwa yanda zasu hada kai don samun riba a kasuwan gas da duniya.
A ganawarsa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya ce kasashen yankin yammacin Asia ne zasu kula da kuma warware matsalolin tsaron da suke fama da su a yankin ba tare da shigar kasar Amurka ba.