Pezeshkian: Ta’addancin Amurka Da Isra’ila Ne Dalilin Matsalar Makamashi

Shugaban Kasar Iran ya bayyana cewa: Yaƙin da ‘yan Sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan Iran ya kawo cikas ga tsaron makamashi da tattalin arzikin

Shugaban Kasar Iran ya bayyana cewa: Yaƙin da ‘yan Sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan Iran ya kawo cikas ga tsaron makamashi da tattalin arzikin duniya

Shugaban Kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya jaddada bukatar karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen da ke fitar da iskar gas, yana mai cewa hare-haren soji da Amurka da Haramtacciyar kasar Isra’ila suka kaddamar kan Iran ya kawo cikas ga tsaron makamashin duniya da tattalin arzikin kasa da kasa.

A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, Pezeshkian, yayin da yake jawabi a taron koli na 8 na kasashen da ke fitar da iskar gas (GECF), ya yi magana kan ci gaban tattalin arziki da kalubalen da tsaron makamashin duniya ke fuskanta, yana mai cewa ana gudanar da taron ne a daidai lokacin da ci gaban yanki da na kasa da kasa ke haifar da manyan kalubale ga tsaron makamashi.

Ya kara da cewa harin soji da Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka kai wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran – wanda ya faru a lokuta biyu daban-daban yayin tattaunawar siyasa da ake ci gaba da yi – lamari ne mai matukar bakin ciki da hatsari ga tsaron duniya. Wadannan ayyuka, ta hanyar lalata kayayyakin more rayuwa na makamashin kasar da kuma kawo cikas ga watsa makamashi, sun yi barazana ga tsaron makamashin duniya da kuma tattalin arzikin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted