Brazil: Jam’iyyar Bolsonaro Ta Amince Da Nasarar Lula

Tun Lahadi ne, Flavio Bolsonaro ya yi ikirarin "magudi" kuma ya nemi a soke zaben.

Jam’iyyar dan takarar masu ra’ayin mazan jiya Flavio Bolsonaro a Brazil ta amince da sake zaben shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva, a matsayin shugaban kasar, bayan zaben ranar Lahadi wanda shugaban Amurka Donald Trump ya kira da mai cike da”magudi.”

Tun da yammacin Lahadi ne, Flavio Bolsonaro ya yi ikirarin “magudi” kuma ya nemi a soke zaben, wanda aka tsawaita da sa’o’i biyu.

Shi dai Luiz Inácio Lula da Silva ya sake zama shugaban Brazil na wani wa’adin tsawon shekaru hudu, Bayan kada abokin hamayyarsa, Flavio Bolsonaro a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar na ranar Lahadi.

Lula da Silva, ya lashe zaben ne da kusan kashi 51.8% na kuri’un da aka kada yayin da abokin karawarsa dan tsohon shugaban kasa Jair Bolsonaro ya samu kashi 48.2% duk da goyon bayan shugaban Amurka Donald Trump.

Wannan sakamakon a cewar masana ya bayar da shaida bayyananniya kan jajircewar al’ummar Brazil wajen kare dimokuradiyya, ci gaban al’umma, da kuma ikon mallakar kasa.

Wannan shi ne karo na farko tun bayan da Brazil ta koma tsarin zaɓen shugaban ƙasa kai tsaye a shekarar 1989, da ɗan takarar da ya zo na biyu a zagayen farko ya yi nasarar lashe zabe a zagayen karshe. 

A zagayen farko a ranar 4 ga Oktoba, Flávio Bolsonaro ne ya kasance kan gaba da kashi 47.03, yayin da Lula ya samu kashi 45.16.

Tuni zababen shugaban ya fara samun sakonnin taya murnadaga shugabannin kassashen duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted