Harin Da Aka Kai Kasar Jordan Ya Lashe Rayukan Mutane 8

Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin cocin Karak ya kai 8, kuma Amurka ta yi kira ga ‘yan kasarta da ke Jordan da su yi

Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin cocin Karak ya kai 8, kuma Amurka ta yi kira ga ‘yan kasarta da ke Jordan da su yi taka-tsantsan

Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin da aka kai wa cocin Orthodox na Girka a ƙauyen Hammoud da ke Karak a yankin kudancin Jordan ya karu zuwa takwas, bayan da daya daga cikin wadanda suka jikkata ta mutu sakamakon raunukan da ta samu. Jami’an tsaro na ci gaba da bin diddigin maharan.

Ministan Lafiya na kasar Jordan Ibrahim al-Badour ya ce 27 daga cikin kimanin mutane 40 da suka jikkata har yanzu suna karbar magani a asibitoci. Harin ya faru ne lokacin da ‘yan bindiga suka bude wuta na tsawon mintuna da dama kan masu makoki da ke halartar jana’iza a cikin cocin a ranar Juma’a.

Daraktan Tsaron Jama’a Abdullah Al-Maayta ya tabbatar a wani taron manema labarai da ya gudanar a Karak tare da Ministan Harkokin Cikin Gida Mazen Al-Faraya cewa: Ana ci gaba da bincike domin zakulo wadanda suka aikata laifin, yana mai jaddada cewa: Lokaci ya yi da za a tantance ko sunan wadanda suke da alaƙa da ƙungiyoyin da ake zargi da kai harin a ciki ko a wajen Jordan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted