Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Ko da al’ummar Iran za su koma cin ƙasa ne, ba za su sallama ko da taku ɗaya na ƙasarsu ba
Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: “Ko da za su koma cin ƙasa ne saboda tsananin takunkumai akan su sallama inci ɗaya na ƙasarsu, sun gwammace da wannan bakar azabar” ya ƙara da cewa: “Iran tana alfahari da ‘ya’yanta waɗanda suka nuna dabi’unsu ba kawai ta hanyar kalamansu ba, har ma ta hanyar dagewarsu a fagen gwagwarmaya.”
A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran, Shugaba Pezeshkian ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa: “Sattārkhan ya yi gwagwarmaya don cimma manufofin da ya ɗauka don kare Iran da suka cancanci kasar: ‘yanci, bin doka, da kuma alfahari da ƙasa. Iran tana alfahari da waɗannan ‘ya’yanta; maza waɗanda suka nuna dabi’unsu ba kawai ta hanyar kalmominsu ba, har ma ta hanyar dagewarsu a fagen kalubalantar makiya.”
Shugaban ya kammala da cewa, “Sun gwammace su ci ƙasa maimakon su mika kasarsu ga wasu munanan azzalumai marasa tarbiyya da sanin kimar dan Adamtaka.”