Baghaei: Lokacin Jinkirin Maida Martani Yace, Doka Da Duka

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baqei ya bayyana cewa lokacin maida martani daga baya kuma ya wuce tsakanimmu da makiya, babu wani hari

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baqei ya bayyana cewa lokacin maida martani daga baya kuma ya wuce tsakanimmu da makiya, babu wani hari da zasu kawowa kasar face mun maida martani a take.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Baghaei yana fadar haka a safiyar yau Talata, a taro da yan jaridu da ya saba gabatarwa a ko wace ranar Talata a ma’aikatar harkokin wajen kasar.

Dangane da sabbin barazanar Amurka na sake farwa kasar Iran da yaki kuma, Baghaei ya ce, mu muna kare mutunci da kuma hakkin mutanen kasar Iran ne, don haka muna jiran duk wata talaka daga kasashe makiya zasu ga abinda zamu iya yi, don kare muradummu.

A wani wuri a jawabinsa kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa rufe mashigar kan iyaka na Pakistan da Iran da aka yi a makon da ya gabata, saboda matsalolin aiki ne kawai, kuma tuni an kauda matsalolin an kuma koma kamar yanda aka kafin haka.

Kafin rufewar dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa sai ya rufe dukkan hanyoyin shiga kasar Iran ta kasa. Bayan ya bada sanarwan rufe ta jiragen sama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted