MDD Ta Rage Taimakon Da Take Ba Falasdinawa 700,000

hukumar kula da abinci ta majalisar dinkin duniya ta rage taimakon da take bawa falasdinawa 700,000

hukumar kula da abinci ta majalisar dinkin duniya an tilasta mata rage yawan taimakon abinci  da take bawa falasdinawa sama da 500,000 a yankin Gaza da kuma 200,000 a gabar yammacin kogin Jodan da aka mamaye saboda karanci kudi da take fuskanta ,inda tayi gargadin cewa rayuwa a yankin gaza tana cikin mummuan bala’i

Carl SKAU daraktan rikon kwarya na hukumar WFP yace adadin mutane dake samun taimako a yankin gaza ya ragu a wannan watan daga mutane miliyan 1.6 zuwa miliyan 1.1, yayin da a yammacin kogin jodan adadin yakai 400,000 zuwa 200,000, don haka yayi kira ga majalisar dinkin duniya da ta samar da dala miliyan 450 cikin gaggawa saboda cibiyar ta ci gaba da aiyukanta har na tsawon watanni 6 masu zuwa.

kamar yadda ta bayyana an rage abincin da ake badawa a yankin gaza zuwa rabi, iyalan da suke ci gaba da samun tallafi za su rika samun kunshi abinci guda daya ne maimakon biyu da suka samu a baya, da karamin buhun flawa.

yace yanayin da ake ciki ya kara Kamari ne bayan takurawar da isra’ila ke yi inda a makon jiya sojojin isra’ila sun dakatar da shigar da kayayyakin kasuwanci na wucin gadi  da suka hada da kayan abinci a yankin gaza, kafin daga bisani ta sanar cewa zaa yi aiki tare game da batun zirga-zirgar manyan motoci na kasauwanci, sai dai tayi gargadin cewa idan aka samu rahoton cewa yan kasuwan sun biya haraji ga shugabannin falasdinawa zai jawo a soke takardun izinin da aka bayar

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted