Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta gayyaci jakadan dake wakiltar kungiyar tarayyar turai wato EU da kuma jakadan kasar Jamus a nan birnin Tehran domin nuna rashin amincewarta da jerin zarge-zarge mara tushe da suka yi wa kasar iran
jakadan kasar Irish a nan Tehran Aidan Cronin wanda ke rike da shugabancin kungiyar tarayyar turai an aike masa da goron gayyata daga Alireza Yousefi darakta a bangaren kasashen turai a majalisar harkokin wajen kasar iran, a jiya litini, kuma yusefi yayi watsi da zargin da aka yi wa iran a takardar bayan taron da aka fitar a taron da kungiyar tayi na tsakiyar Oktoba, inda ya nuna cewa yanayin da ake ciki yanzu a yammacin asiya da tekun pasha, sakamakon manufofin kungiyar EU ne na rashin daukar nauyi da kuma goyon baya kai tsaye da na fakaice da wasu kasashen kungiyar suka bayar ga gwamnatin amurka da israila a harin da suka kaiwa kasar iran
haka zalika babban jami’in diflomasiyar na kasar iran ya bayyana cewa dole ne kungiyar EU ta dauki alhaki game da bin siyasar amurka kan shirin nukiliyar iran ido rufe wanda aka ce yayi mummunan illa ga tsarin hana yaduwar makamai masu linzami na duniya kana kuma ya bayyana zargin da ake yi wa iran a kasar jamus a matsayin wata dabara ce da wasu jami’ain kasashen turai ke amfani da ita don boye goyon bayan da Berlins ta bawa Amurka da Isra’la kan hari da suka kai wa kasar Iran