Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar iran mas’ud pezeshkiyan yace tsare-tsaren Washington ya jefa yankin cikin rashin zaman lafiya, kuma yayi gargadin cewa kasancewar sansanonin kasar Amurka a yankin ya taimaka sosai wajen ruruta rikici da rashin zaman lafiya da tsaro,
Pezeshkiya yayi wannan bayanin ne a jiya litinin a lokacin ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar rasha Sergei Lavrov da yake ziyarar Aiki a nan iran inda yake jagorantar babbar tawagar diflomasiya domin tattaunawa kan sabbin abubuwa da suka shafi yankin da ma na duniya baki daya
haka zalika ya kara da cewa shahadar jagoran juyin musulunci na iran da sauran kwamandojin soji da masana ilimin fasaha da daliban makaranta da kuma kai hari kan muhimman abubuwan more rayuwa na alumma a yakin da Amurka da isra’ila suka kaddamar kan kasar iran ya sabama dokokin kasa da kasa
Ana shi bangaren lavrov ya jaddada matsayin mosko na kara karfafa dangantakarta tsakaninta da kasar iran,yace kasashen biyu za su ci gajiyar juna a bangaren man fetur da iskar Gas, sadarawa da kuma musayar ala’adu , sufuri, da kuma yin aiki tare a bangaren jamio’i