Gwamnatin San’aa ta sanar da cewa sojojinta sun kai hari akan ‘yan koren Saudiyya a garin “Ta’iz”.
Sojojin na Yemen sun yi amfani da jirage marasa matuki wajen kai hare-haren a sansanonin ‘yan koren Saudiyya, kamar kuma yadda aka ji karar fashewar wasu abubuwa masu karfi a cikin garin na Ta’iz.
Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani akan hakikanin abinda ya faru da ya haddasa karar fashewar abubuwa a cikin garin na Ta’iz.
Gwamnatin Sanaa tana son ganin Saudiyya ta dauke takunkumai da killace ta da ta yi na shekaru masu tsawo tare da yin aiki da yarjejeniyar sulhu da su ka cimmawa a kasar Oman.