Amurka Ta yi Watsi Da Bukatar Saudiya Na Jagorantar Yaki

kasar amurka take amincewa ta taimakawa saudiya ta jagorancin yaki da yan huthi

Jami’an sojin Amurka sun yi watsi da bukatar da gwamnatin Saudiya ta gabatar musu na  jagorantar matakin soji da take son dauka kan kasar Yamen adaidai lokacin da sojojin kasar Saudiya suka kasa tunkarar dakarun gwagwarmaya na kungiyar Ansarullah

Kafafen yada labaran isra’ila sun bayyana cewa wani da ya bukaci a sakaya sunansa yace a ranar Asabar yarima mai jiran gado na saudiya mohammad bin salman ya bukaci kwamandan yaki da taaddanci na Amurka CENTCOM admiral brad cooper da ya jagoranci matakin soji da take son dauka kan kasar Yamen

Martanin da Amurka ta bayar shi ne za ta iya taimawa sojojin kasar Saudiya amma ba za ta jagoranci rundunar ba , ganin cewa har yanzu dakarun sojin yaman ba su kai hari kai tsaye kan sojojin Amurka ba a tekun bahar maliya sun mayar da hankali ne kan jiragen ruwan kasar Saudiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted