Babban sakatare janar din kungiyar hizbullah ta kasar Labanon shaikh Naim Qasem ya jinjinawa alummar iran game da irin jajirtacewa da ta nuna a yake-yaken da kasar Amurka da isra’ila suka kaddamar a kanta, yana jaddada cewa juriya ta mayar da makiya baya, kuma ta wargaza makirce-makircen da suke kullawa
A lokacin da yake jawabi a wajen taron makon hadin kai yace kasashen Amurka da Isra’ila sun sha kashi a yake- yake guda 3 da suka kaddamar akan kasar Iran sakamakon nuna tsayin daka da jajircewa da hadin kai da alummar kasar suka nuna, wato yakin da Amurka ta kaddama a watan yuni shekara ta 2025 da kuma watan fabarerun shekara ta 2026 kafin daga bisani kuma ta kara kaddamar da hari a watan yuli
Haka zalika ya nuna cewa matukar muka tsayan kam wajen kare hakkinmu da kasarmu makiya ba za su iya cimma burinsu ba, duk irin sadaukarwa da za mu yi da kuma adadin mutane da za’a kashe , yace rashin jituwa tsakanin gwamnatocin musulmi bai kamata ya bude wani sabon babi a cikin gida ba, da zai sanya su manta da manyan abokan gabansu ba
Shaikh Naim Qasem ya nuna cewa jagoran juyin musulun na iran Ayatullah Sayyid Ali Khamna’I ya canza tsarin hadin kan musulmi zuwa hadin kai a aikace, sannan kuma ya sake farafado da batun falaasdinu a matsayin babban matsala ta duniya musulmi.