Jagora Ya Bukaci Hadin Kan Musulmi

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Sayyid Aya. Mojtaba Ali Hussaini Khaminaei ya bayyana cewa kasashen yan ta’adda Amurka da HKI basa kaunar

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Sayyid Aya. Mojtaba Ali Hussaini Khaminaei ya bayyana cewa kasashen yan ta’adda Amurka da HKI basa kaunar musulmi gaba daya a ko ina suke.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a sakon da ya aikawa mahallata taron hadin kai tsakanin musulmi shia da sunnan a nan birnin Tehran. Ya kuma kara da cewa, wadannan makasa makiya baya boye kiyayyarsu ga musulmi gaba daya, ba iraniyawa kadai ba.

Aya. Khaminaei ya yi kira ga shuwagabannin kasashen yammacin Asia da kuma na yankin tekun farisa da su gane makiyansu su kuma fuskancesu. Yace HKI da Amurka ba masoya bane, kuma hadin kai tsakanin musulmi shi ne mafita.

Ya bayyana cewa, Amurka da HKI basa boye kiyayyarsu ga al-ummar musulmi don haka bai kamata ace wasu shuwagabnnin musulmi su yi kawance da su ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted