Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baqaei ya yi ba’a ga shirin Amurka na kara takurawa kasar Iran na baya bayan nan, ya ce wannan ya nuna gazawarta wajen samarda kawance kasashe wadanda zasu yi adawa da kasar sa.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalyo Baqaei ya ba’a ga Amurka a wani sakon da ya aiki a shafinsa na X a yau Alhamsi, ya kuma da cewa: Sanya kasar Bahrain cikin kasashen da suke goyon bayanta a wannan shirin, ya zama barkwanci inda take bukatar kasar Bahrain ta yanke huldar kasuwanci da wasanni da Iran, Bahrain wacce bata da wani harkar kasuwanci na kirka da Iran na shekaru masu yawa, me zata iya yi.
Ya ce: babu wani harkar kasuwanci, ko wasanni ko kuma musayar ilmi da kasar Bahrain na tsawon shekaru masu yawa. Yace Amurka tana dorawa kasa wacce dama tana cikin takunkuman Amurka, sannan tana kiran haka kawancen kasashe.
Baqaei ya yi wannan bayanin ne bayan da sakaren baitul malin Amurka Scott Bessent ya bada sanarwan samar da shirin takunkuman tattalin arziki kan kasar Iran wanda ya sanyawa suna ‘Shirin Share tattalin arziki’.