Aragchi Ya Bukaci MDD Ta Yi Allawadai Da Takunkuman Amurka

Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Aragchi, a cikin wata wasikar da ya rubutawa MDD ya bukaci majalisar ta yi allawadai da takunkuman ta’addancin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Aragchi, a cikin wata wasikar da ya rubutawa MDD ya bukaci majalisar ta yi allawadai da takunkuman ta’addancin da Amurka ta dorawa JMI a baya bayan nan. Ya ce wannan shi ne yakamata tayi a shari’anci da kuma hankali.

Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa ministan ya fadawa kamfanin dillancin labaran Mehrnews kan cewa shirin Amurka na kakabawa Iran sabbin takunkuman tattalin arziki, shirin na aikin ta’addanci, sannan bayan haka ta sha alwashin hukunta duk wata kasa a duniya wacce ta sabawa umurninta, ta kuma ki yanke huldar kasuwanci da Iran. Ta yi barazanar hana duk kasar da ta yi haka, daga tsarin kudade na bai daya a duniya.

Aragchi ya kara da cewa, bayan da Amurka ta kasa cimma burinta na kifar da gwamnatin JMI a yake-yake guda biyu a shekara 2025 da 2026, da kuma gazawarta wajen jawo wasu kasashe su taimaka mata kan ayyukan ta’addanci da take a kasar Iran daga karshe ta sake dawowa kan takunkuman ta’addanci, inda take fatan zata cimma abinda ta gaza samu a yake yake.

Wasikar ta bukaci majalisar ta yi allawadai da tir da Amurka kan wadannan ayukan sabawa doka. Rashin haka zai sanya ayar tambaya a cikin ayyukan MDD. Kuma rashin magana a kan wadannan al-amura ya sabawa doka da ka’idoji na majalisar dangane da yencin kai dai daito kamar yanda ya zo a doka ta 2 (1) ta majalisar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted