Shugaban kasar Iran Dr. Mas’ud Pezeshiyan ya fada a yau Alhamis cewa; Kasashen Amurka da ‘Yan Sahayoniya sun shelanta yaki akan Iran adaidai lokacin da ake kan ganiyar tattaunawa.
Shugaban kasar ta Iran ya kuma kara da cewa: Iran ba ita ce ta fara yaki ba, abinda mu ka yi shi ne tsayawa da karfi a gaban masu wuce gona da iri, mu ka kuma kare kawukanmu.”
Haka nan kuma shugaban kasar ta Iran ya ce; Mun yi Imani da cewa kare Falasdinu da kin amincewa da mamaya, wani abu ne da yake wajibi akanmu.”
Haka nan kuma shugaban kasar ta Iran ya ce; Wajibi ne ga kasashen musulmi da su yi aiki a tsakaninsu, su kuma yi alkawalin rashin cutar da ‘yan’uwansu.”
Bugu da kari shugaban kasar ta Iran ya ce; Al’ummar Iran sun hade sun zama tsintsiya daya lokacin da tsaron kasarsu ya fuskanci matsala,duk kuwa da cewa suna da sabani a tsakaninsu.”
Shugaba Pezeshkiyan ya kara da cewa; A matsayinmu na kasashen musulmi ya zama wajibi a gare mu ya zama muna ‘yancin daukar matakai akan manufofin da mu ka yi tarayya akansu, ba tare da bakin haure sun tsoma baki ba.