Iran Ta Mika Taaziyya Da Pakistan Kan Mutuwar Jarirai 14 A Asibiti

jarirai 14 ne suka mutu bayan gobara ta tashi a wani asibiti a pakistan

kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran isma’ila baqaka’i ya  aike da sakon gwamnatin iran da alummar kasar na ta’aziyya ga alumma da gwamnatin  Pakistan na mutuwar wasu jarirai sabbin haihuwa guda 14 sakamakon tashin gobara a wani Asibiti a kasar ta pakistan

Asibitin Pakistan Institute of Medical Sciences da ke Islamabad yana dauke da akalla jarirai 15 a dakin kula da jariran lokacin da gobarar ta tashi, Jami’ai sun ce an samu nasarar ceto jariri guda, yayin da Ministan Lafiya na Tarayya, Mustafa Kamal, ya tabbatar da cewa akalla jarirai 14 sun rasu.

Jami’an ceto sun ce gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 6:45 na safe, bayan da na’urar sanyaya daki ta fashe a cikin dakin jariran da ke sashen kula da mata masu juna biyu da masu haihuwa.

Daga bisani, Babban Kwamishinan Islamabad, Suhail Ashraf, ya ce an kashe gobarar gaba daya, kuma hukumomi na tattaunawa tare da iyalan jariran. kuma tuni fira ministan Pakistan ya bada uamarnin gudanar da bincike abin da ya jawo tashin gobarar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted