Iran Ba ta Bukatar Izinin Kowa Wajen Kulla Dangantaka Da China

babu bukatar iran ta nemin izinin wani don kulla dangantaka da kasar china

Kakakin majalisar shawara ta kasar iran mohammad Baqer Qalibaf yace yin watsi da sabbin takunkumin da amurka ta kakabawa kasar Iran ya nuna irin kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da ta zarta dagantakar kasa da kasa ta yau da kullum wacce za ta iya yi mata togiya kan kakaba takunkumi ko barazana a akanta

Qalibaf ya fadi acikin shafinsa na X cewa kasashen iran da china za su ci gaba da bunkasa dagantakarsu na tsawo shekaru 25 na yarjejeniyar  da suka kulla tsakaninsu a watan maris din shekara ta 2021,don haka wannan dangantakar bata bukatar izinin kowa,

Wannan yana zuwa ne kwana daya bayan da ministan harkokin wajen kasar China ya bayyana cewa baijin  zai yi duk abin da zai yi  na wajibi wajen kare hakkin kasar china, da kuma manufofita bayan da Amurka ta sanar da sanyawa iran sabon takunkumi tattalin arziki  da ta kira shi da D-Day, wani yanayi da Washington ke son nuna irin matakin nuna adawa da kasar iran

Haka zalika ya kara da cewa hadin guiwa dake tsakanin iran da china yayi daidai da dokokin kasa da kasa don haka china tana adawa kai tsaye da takunkumin da aka sanya wa iran da ya sabama dokokin kasa da kasa ko kuma kudurin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted