Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran wanda ya kai ziyarar aiki kasar Iraki ya gana da Fira minister Ali Falih al-Zaydi,inda su ka tattauna hanyoyin bunkasa alakar kasashen biyu.
Haka nan kuma Muhammad Bakir Kalibaf ya gana da jami’an gwamnatin kasar ta Iraki da su ka hada da mai bayar da shawara akan harkokin tsaro kasa Kassim Abbudi.
Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf ya kuma ce; Alaka a tsakanin Bagadad da Tehran tana da matukar muhimmanci a cikin wannan yanakin na sauyin da ake samu a wannan yankin,tare da cewa; Wannan yankin zai shiga a karkashin wani sabon tsari.
A gefe daya, shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran zai kuma ziyarci birnin Karbala inda za a yi taron cika kwanaki 40 daga jana’izar jagora shahidi Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ( q.s)