Rahotanni sun bayyana cewa sabbin kwamandojin dakarun kare juyin musulunci na kasar da jagoran juyin musulunci ya nada a jiya talata sun sha alwashin cika burin jagora Ayatullah sayyid Mojtaba Khaman’I ga dakarun sojin kasar
Major Janaral Ahmad Vahidi yayi wannnan bayanin ne a wani sakon da ya aiki da shi a jiya talata ga major janaral Ali Abdullahi inda yake taya shi murna game da nadin da akai masa a matsyin kwamandan hafsan hafsoshin sojin kasar iran,
Wannan nadi ya zo ne a ranar litinin bayan da jagoran juyin musulunci na iran Ayatullah Khamenei ya sanar da karawa Vahidi mukami zuwa major janaral kuma ya nada shi a matsayin kwamandan dakarun kare juyin musulunci na kasar daga ciki jerin nade-naden da yayi a bangaren soji, kuma ya sha alwashin yin tsayin daka ga zalunci Amurka da isra’ila da kuma aiki da taken iran mai karfi da tsarin rundunar kare juyin musulunci.
A wani sako na daban, kwamadan ya taya birgediya janar Kiomars haydari murnar nada shi da aka yi a matsayin mataimakin kwamandan hafsan hafsoshin sojin kasar da jagora yayi, haka zalika a cikin wasikar yayi ishara ga wasu bukatu da jagora sayyid Mujtaba Khamna’I yake da shi ga dakarun sojin kasar wanda zai taimaka wajen karfafa tsaro da zaman lafiya, da kuma karfafa sojojin wajen bangaren ma’anawiya