Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta haramta wucewar kayayyakin Amurka da na ‘yan sahayoniyya ta mashigar ruwar Hormuz
Kakakin kwamitin harkokin cikin gida da na kananan hukumomi na Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya tabbatar da cewa, a yayin taron da suka gudanar a yau, kwamitin ya amince da haramta wucewar kayayyaki da na’urori mallakar Amurka, da gwamnatin Yahudawan Sahayoniyya da kuma kasashen da ke gaba da Iran ta cikin Mashigar Hormuz.
Waliyyullah Wulayati kakakin kwamitin, ya bayyana cikakkun bayanai game da taron da aka gudanar a yammacin ranar Litinin, inda ya ce: “Taron ya tattauna dalla-dalla kan wani shirin aiki mai muhimmanci da nufin tabbatar da tsaro mai dorewa a Mashigar Hormuz da Tekun Fasha. Wakilai daga gwamnati, da Ma’aikatar Harkokin Waje, da kuma Babban Hedikwatar Sojoji sun halarci taron, tare da jami’an zartarwa masu ruwa da tsaki da kuma kwararru daga Cibiyar Bincike ta Majalisar Shawarar Musulunci.”
Ya bayyana cewa an riga an amince da muhimman abubuwan da kudirin ya kunsa a yayin taron kwamitin da ya gabata, inda ya ce: “A taron na yau, ‘yan majalisa sun tattauna kan sassa biyar na kudirin; bayan tattaunawa da musayar ra’ayoyi, daga karshe mambobin kwamitin sun amince da su.”