Aragchi Ya Tattauna Da Tokwaransa Na Pakistan Kan Yankin

Ministan harkokin waje na kasar Iran Abbas Aragchi ya tattauna ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Pakistan Mohammad Ishaq Dar dangane da yarjeniyar da

Ministan harkokin waje na kasar Iran Abbas Aragchi ya tattauna ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Pakistan Mohammad Ishaq Dar dangane da yarjeniyar da kasarsa ta cimma da kasar Omman kan mashigar ruwa ta Hurmuz.

Kamfanin dillancin labaran Mehr News na kasar Iran ta bayyana cewa a na shi bangaren Dr ya yiwa Aragchi karin bayani kan yarjeniyar tsaro ta Macca wacce kasarsa da Turkiyya da kuma kasar Saudia suka sanyawa hannu a cikin kwanakin da suka gabata. Yace manufar yarjeniyare karfafa harkokin tsaro a yankin ne.

Bangarorin biyu har’ila yau sun tattauna dangane al-amura da suka shafi tsaron yammacin Asiya gaba daya, da kuma hanyoyin dawo da zaman lafiya a yankin bayan hare hare wanda babu tsokana a cikinsa wanda Amurka da HKI suka farwa kasar Iran da su.

Aragchi ya yiwa Dar karin bayani dangane da yarjeniyar Iran da Omman kan zirga zirgan jiragen ruwa a mashigar a duk lokacinda aka bude ta, sannan matsayin JMI dangane da bude ta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted