Amurka: Sanatoci 11 Sun Bukaci Amurka Ta Dakatar Da Yaki Da JMI

Sanatoci 11 daga jam’iyyar Democrat a Majalisar Dattawan Amurka sun bukaci gwamnatin Donald Trump ta dakatar da yaki da JMI tare da takaita ikon shugaban

Sanatoci 11 a majalisar dattawan Amurka sun bukaci gwamnatin shugaba Trump ta kawo karshen duk wani yaki da JMI.

Kamfanin dillancin Tasnim na kasar Iran ya nakalto kafafen yada labaran kasar na cewa, sanatocin kasar 11 daga jam’iyyar Democrates sun gabatar da da wani kuduri wanda ya bukacin gwamnatin kasar ta dakatar da yaki da JMI, sannan a takaita hakkin shugaban kasar na shiga yaki ba tare da amincewar majalisar dokokin kasar ba.

Labarin ya kara da cewa, janar janar na sojojin Amurka, bayan gazawarsu a fafatawa da sojojin JMI suna neman hanyoyin ficewa daga yakin. Har’ila yau majalisar dokokin kasar tana neman hanyoyin takaita karfin shugaban kasa na shiga yaki da kasar Iran ba tare da amincewar majalisun dokokin kasar ba.

Wannan matsalar ta jawo sabani mai tsanani tsakanin fadar shugaban kasa da kuma majalisun dokokin kasar, wacce take bukatar daga yanzu dole ne shugaban ya nemi amincewar majalisar dokokin kasar kafin duk wani yaki da zai shiga ko ci gaba da JMI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted