Shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan ya gargadi kasar Amurka da sauran kasashen duniya kan yiyuwan Amurka ta sake amfani da makaman nukliya kan wata a kasa a duniya.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau a shafinsa na X, ya kuma bayyana haka ne a dai dai lokacinda ake tunawa da makaman nukliyan da gwamnatin Amurka ta yi amfani da su kan kasar Japan a shekara 1945.
Shugaban ya kara da cewa, a halin yanzu da alamun Amurka zata iya maimaita wannan ta’asar a kan wata kasa ko kasashe a duniya.
Yace ‘ a dai dai lokacinda ake juyayin boma boman Nukliyan da Amurka ta jefa kan biranen Nagasaki da Hiroshima na kasar Japan a ranakun 6 da kuma 9 na watan Augustan shekara 1945, dole ne kasashen duniya su yi tir da kasar Amurka a irin wannan halin da ke ciki a duniya, yane hakan ba zai sake faruwa ba.
Banda kissan dubban mutane da makaman suka yi a kasar Japan sun gurgunta rayuwar mutane da dama, sun kuma bar tasirin guban da ke cikin makaman yana cutar da mutanen kasar har yanzun da muke magana.
Ana juyiyin ranakun jefa makaman nukliya a kan kasar Japan a duniya a ko wace shekara, dun tunawa da musiba babba da ta sami duniya a wancan lokacin da kuma fatan ba za’a sake yin haka a duniya ba.