Kamfanin dillancin “AFP” ya ambato wata majiya ta kasar Yemen din tana cewa,sanadiyyar harin da aka kai daga Sanaa, adadin wadanda su ka rasa rayukansu ya karu zuwa 58.
A tashin farko, runduna ta daya ta sojojin da Saudiyya take goyawa baya,ta sanar da cewa adadin sojojin da su ka rasa rayukansu sanadiyyar harin na gwamnatin Sanaa sun kai 30.
An kai harin ne dai akan sansanonin soja a gundumomin “Hadhara-maut’ da kuma Ma’arib.
A can birnin Sanaa, kakakin soja Janar Yahya Sari ya sanar da cewa sun kai harin ne a jiya Alhamis akan sojojin Saudiyya da suke taruwa a yankunan “Ruwaik” da ‘Al-Ibr’ da kuma “al-Saniyyah” da kuma wasu sansanonin soja a runduna ta farko da ta uku.
Janar Sari ya ce sun yi amfani da makamai masu linzami ne wajen kai hare-haren, haka nan kuma jiragen sama marasa matuki, bayan da su tabbatar da bayanai akan haduwar sojojin da zummar kai wa yankunan Yemen ‘yantattu hare-hare.
Janar Sari ya ce; manufar shirya wannan harin shi ne hana Yemen ci gaba da aiwatar da killace jiragen ruwan Saudiyya da su ka yi domin dauke wa Yemen takunkumin da su ka kakaba mata.
Wani jami’i na kungiyar Ansarullah Muhammad Shaukah ya ce harin nasu na kandagarko ne domin dakile da hana harin da Saudiyya ta shirya kai wa Sanaa.
Makwanni kadan da su ka gabata ne dai gwamnatin Sanaa ta sanar da cewa ta hana jiragen ruwan saudiyya wucewa ta mashigar Babal-Mandab, har sai idan an dauke mata takunkumin da Saudiyyar ta kakaba mata .