Sheikh Kassim: Gwgawarmaya Za Ta Ci Gaba Matukar Da Akwai Mamaya

Har ila yau babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya ce; Mun yi Imani da Lebanon a matsayin kasa daya dunkulalliya wacce babu yadda za a
Sheikh Nassim Kassim

Baban magatakardar kungiyar  ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim  wanda ya gabatar da jawabi a ranar Arba’in na shahadar Imam Hussain ( a.s) ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta daina mika wa “Isra’ila” kai da yi ma ta sasauci cikin sauki.

Haka nan kuma Sheikh Na’im Kassim ya yi kira ga gwamnatin ta Lebanon da ta bude tattaunawa da gwgawarmaya,sannan kuma ya kara da cewa:Gwagwarmaya za ta cigaba matukar da akwai mamaya.”

Har ila yau babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya ce; Mun yi Imani da Lebanon a matsayin kasa daya dunkulalliya wacce babu yadda za a iya raba ta, ko kuma a yi sassauci akan taku daya nata.”

Sheikh Na’im Kassim ya ce; Isra’ila ba ta da wani zabi a gabanta da ya wuce ta fice daga cikin kasar ta Lebanon, kuma dole ne ma zai fice.”

Sheikh Na’im Kassim ya ce, manufar da ‘yan sahayoniya su ka sanya a gaba ita ce tun a cikin watan Satumba na 2024 shi ne kawo karshen gwagwarmaya daga kasar Lebanon.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma yi bayani akan yadda su ka fuskanci ‘yan mamaya, su ka kuma ci gaba da gwagwarmayar da ta tilastawa wa ‘yan sahayoniya amincewa da yarjejeniya hakkin yin gwgawarmaya.

Sai dai kuma bayan gushewar watanni 15, yan sahayoniyar sun yi amfani da dukkanin hanyoyi domin ganin bayan gwgawarmaya. Sun zaci cewa za su murkushe gwagwarmayar, to amma sun yi mamaki akan yadda su ka ci karo da karfin gwagwarmaya.

Da yake Magana akan alakar kungiyar ta Hizbullah da kasar Syria, Sheikh Na’im Kassim ya ce, babu laifi idan aka yi ganawa a tsakaninsu da gwamnatin Syria a lokacin da ya dace.

Sheikh Na’im Kassim ya ce babu wani abu da zai hana a yi ganawa a tsakanin kungiyar Hizbullah da shugabannin kasar Syria a lokacin da yanayi ya bayar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted