Iran Ta Kira Jakadan Burtaniya A Tehran Dangane Da IRGC

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a nan Tehran ta kira jakadan kasar Burtania a nan Tehran zuwa ma’aikatar don gabatar da korafinta kan yanda gwamnatin

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a nan Tehran ta kira jakadan kasar Burtania a nan Tehran zuwa ma’aikatar don gabatar da korafinta kan yanda gwamnatin kasar Burtania ta zayyana dakarun kare juyin juya halin musuluncin kasar Iran wato IRGC a matsayin kungiyar yan ta’adda tare da gabatar da hujjoji na karya.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar ma’aikatar tana cewa, mataimakin ministan harkokin waje mai kula da kasashen yammacin turai wato Alireza Yusufi ne ya kira jakadan London a Tehran Hugo Shorter zuwa ma’aikatar a jiya inda ya gabatar masa da korafin a zaman da yayi da shi.

Yusufi ya yi allawadia da jawabin sakataren harkokin cikin gida a majalisar dokokin kasar Burtaniya wadanda suke sukan JMI, wanda bai kamata a ce gwamnatin kasar Burtania su amince a yi wannan sukar ga kasa wacce take da huldar jakadanci da it aba. Jawabinda majalisar dokokin ta gina a kansa ta kuma amince a sanya dakarun IRGC cikin kungiyoyin yan ta’adda a wajensu.

Daga karshe Yusufi ya kammala da cewa duk wani kokari na taba tsaro da mutuncin kasar Iran daga bangaren Burtania ko wata kasa a duniya zai gamu da maida martani mai tsanani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted