Dakarun IRGC sun sanar da rufe mashigar ruwan Hurmuz da hana jiragen ruwa wucewa tare da yin gargadi da cewa za ta mayar da martani ga duk wani sabon wuce gona da iri.
Rundunar ruwa ta IRGC ta bayyana cewa; a baya mun yi gargadin cewa duk wani kokari na dawo da kai da komowar jiragen ruwa ba bisa doka ba, zai fuskanci mayar da martani mai karfi.
Sanarwar ta kuma ce, a sa’o’in da su ka shude wasu jiragen ruwa sun yi kokarin wucewa ta wata hanya ta daban a karkashin zugar wasu kasashen waje,tare da yin watsi da gargadin da aka yi musu.
Bugu da kari sanarwar ta IRGC ta bayyana cewa; Wani daga cikin jiragen ruwa ya rufe na’urar da ake iya bibiyarsa, da hakan yake jefa tsaron ruwan cikin hatsari, lamarin da ya sa aka bude masa wuta. Bayan wannan abinda ya faru ne, rundunar ruwan ta dakarun IRGC su ka sanar da rufe mashigar ruwa, da hana duk wani jirgin ruwa ratsawa har illa masha Allah.