Mai bayar da shawara ga jagoran juyi ta fuskar soja, Muhsin Ridha’i ya bayyana cewa; Za mu ci gaba da sarrafa mashigar ruwan Hurmuz, kuma abinda yake gaban Iran shi ne daukar fansa.
Janar Muhsin Rhidha’i wanda ya halarci zaman juyayi na girmama jagora shahid da aka yi a garin Bajnurd, ya bayyana sakon jagora na yin godiya da jinjina ga mutanen Khurashan ta Arewa yana mai cewa; Mutanen wannan gundumar sun shiga an yi da su wajen jana’izar jagora shahidi haka nan kuma a cikin tarukan girmama shi.”
Janar Muhsin Ridha’i ya kuma ce, jagoran juyin musulunci ya aiko shi da sakon yin godiya ga mutanen yankin da jami’ansu.
Haka nan kuma ya bayyana taron jana’izar da cewa shi ne mafi girma a tsawon tarihi,wanda kuma duniya ta kalle shi da bayana shi cike da mamaki.
Da yake Magana akan matsayar Amurka kuwa, Muhsin Ridha’zi ya ce; Yadda aka gabatar da jana’izar jagoran juyin ya bakantawa abokan gaba amma wannan bai dada al’ummar Iran da kasa ba, za su ci gaba da tafiya akan tafarkinsu, bisa dogaro da Imani da kuma hadin da kare