Algeria da Mali sun sanar da cewa za su bude sararin samaniyarsu ga jiragen saman junansu, inda suka mayar da jakadunsu, abin da ke nuni da dawowar danganta bayan kwashe watanni 15 ana tankiyar diflomasiyya.
Dangantakarsu ta yi tsami a cikin ƴan shekarun baya-bayan nan, musamman tun bayan da sojoji suka karbe mulki a kasar Mali kana suka zargi Algeria da katsalandan a cikin harkokin da ya shafin cikin gidanta.
Sanarwar ta kuma bayyana aikewa da jakadanta, wanda tun a watan Afrilun shekarar 2025 aka janye shi, sai dai babu takamammen ranar da aka sanya don aiwatar da hakan.
Tun da farko Algeria ta fitar da makamncin sanarwar da Mali ta fitar a game da bude sararin samaniya a tsakaninsu, wanda ta ce matakin zai fara aiki ne daga ranar Juma’a. Kamar dai yadda Mali ta yi, Algeria ma ta sanar da komawar jakadanta zuwa kasar Mali.