Ibrahim Nakha’i: Iran Za Ta Mayar Da Martani Mai Karfi Akan Duk Wata Wautar “Isra’ila”.

Dan majalisar Iran Ali  Asgar Nakha’i ya shaida wa tashar talabijin din al-mayadeen cewa; Har yanzu Iran ba ta yi aiki da cikakken karfin da 

Dan majalisar Iran Ali  Asgar Nakha’i ya shaida wa tashar talabijin din al-mayadeen cewa; Har yanzu Iran ba ta yi aiki da cikakken karfin da  take da shi na makamai masu linzami ba, tare da yin gargadin cewa; Idan wani sabon fadan ya sake barkewa to makiya za su kasar da za ta shiga tarihi.

Dan majalisar na Iran ya kuma yi Ishara da yadda miliyoyin mutanen Iran su ka halarci jana’izar Jagora Shahid Sayyid Ali Khamenei wacce ta rusa duk wata parpaganda akan Iran, sannan kuma ya ce, mahalarta jana’izar sun aike da sakonsu akan cewa; suna son a dauki fansar jinin jagoransu.

Haka nan kuma ya ce; Amurka ba za ta iya komawa yaki ba, kuma da Zarar Iran ta mayar da martani akan hare-haren da aka kawo mata,to Amurkan za ta ja da baya.

Nakha’i ya kuma yi Magana akan yiyuwar “Isra’ila” ta kawo wa Iran wani harin inda ya ce, martanin da Iran za ta mayar zai zama mai tsanani.

A gefe daya dakarun kare juyin musulunci na Iran sun sanar da mayar da martani akan hare-haren Amurka, tare da jaddada cewa,sun kai hari akan cibiyar sojan Amurka dake yammacin Asiya da cibiyar dake garin “Azraq” dake kasar Jordan ta hanyar harba makamai masu linzami samfurin “Ballastic” 10 da misalin karfe 2:00 na daren Alhamis.

 Iran dai ta mayar da martani ne akan wuce gona da irin Amurka na kawo hare-hare a yankunan kasar da dama wanda yake a matsayin keta yarjejeniyar fahimtar juna ta tsagaita wuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted