A Iraki Miliyoyin jama’a ne suka hallara a biranen Najaf da Karbala don jana’izar ban kwana da Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Seyyed Ali Khamenei.
Rundunar Hashd al-Shaabi, ta Iraki, ta ce sama da mutane miliyan 2.3 ne suka halarci jana’izar a Najaf.
A wani labarin kuma, gidan talabijin na Al Mayadeen, wanda ya ambato gwamnan Karbala, ya ruwaito cewa hukumomi sun yi rijistar mutum miliyan 7 a Karbala.
Tun kafin wayewar gari, masu makoki sun yi ta kwarara zuwa Najaf daga ko’ina cikin Iraki, inda rahotanni suka bayyana taron a matsayin wanda ba a taba ganin irinsa ba.”
Jana’izar a Iraki ta biyo bayan wacce aka gudanar a biranen Tehran da kuma Qom na Iran a ranar Litini da kuma Talata.
An yi kiyasin cewa mutane kimanin miliyan ashirin suka halarci tarurukan jana’izar a Iran.
A gobe Alhamis ne aka tsara dawo ada gazar Shahid Ayatollah Sayyed Ali Khamenei a birnin Mashad domin yi mata ban kwana na karshe tare da binne shi.
Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya yi shahada ne tare da wasu iyalensa da makusantansa a wani harin Amurka da Isra’ila a ranar 28 ga watan Fabarairu a gidansa dake Tehran.